Iyalin wata mata Barira Alhassan na neman ayi adalci tare da gudanar da bincike mai zaman kansa bayan ta yi zargin cewa an cire mata koda daya yayin da ake yi mata aikin tiyata a Asibitin Kwararru na Jihar Gombe.
SolaceBase ta ruwaito cewa wannan zargi ya haifar da damuwa a tsakanin jama’a tare da yin kira da ayi adalci da bayyana gaskiya kan lamarin lafiya, duk da cewa asibitin ya musanta yin wani aiki na tiyata da ya shafi kodar ta.
Barira, wacce ta bayyana hakan a wata hira da BBC News Pidgin, ta ce ayi mata aikin gaggarumin na haihuwa a asibitin a ranar 8 ga Afrilu, 2026, amma bayan kwanaki kadan ta fara fuskantar matsalolin lafiya masu tsanani.
A cewarta, ta fara fuskantar amai ba tare da tsayawa ba, ciwon ciki mai tsanani, kumburin jiki da ciwo yayin fitsari jim kadan bayan an sallame ta daga asibiti.
Mahaifiyar yara goman ta ce wannan shi ne aiki na farko da aka yi mata duk da cewa ta haifi sauran ‘ya’yanta ba tare da tiyata ba.
Ta ce damuwarsu ta kara girma bayan lafiyarta ta ci gaba da tabarbarewa, har sai da daga bisani ta sake ganin wani likitan.
Barira ta yi zargi cewa likitan da ya dubata ya shaida mata cewa tana da koda daya ne kawai, wani lamari da ta bayyana a matsayin mai ban mamaki kuma mai wahalar fahimta.
“Abin da ya fi ba mu mamaki shi ne jin cewa yanzu tana da koda daya kawai,” wani dan uwan ta yana jaddada cewa suna bukatar amsa da adalci.
Iyalin sun ci gaba da zargin cewa bayan sun gabatar da korafinsu ga asibitin, an bukace su da kada su bayyana lamarin ga jama’a.
Dan uwan Barira, Zakaria Alhassan, ya ce shakku ya karu bayan sun duba wani sakamakon binciken yanayin lafiya da aka yi a 2015 wanda ya nuna cewa Barira tana da kododi biyu kafin aikin tiyatar.
A cewarsa, duk kokarin da suka yi na samun bayani mai gamsarwa daga hukumomin asibiti bai yi nasara ba.
Ya kuma ce sun nemi takardun bayanan lafiyar Barira, amma aka shaida musu ba za a iya basu ba.
Saboda rashin gamsuwa da amsar asibitin, iyalin sun mika korafi ga Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Gombe suna neman a yi bincike mai zaman kansa kuma bayyananne.
Zakaria ya ce daga bisani jami’an ma’aikatar sun gayyaci Barira, mijinta da wakilan asibitin zuwa tattaunawa, inda aka ba su shawara su bari a ci gaba da bincike kafin su tattauna lamarin a fili.
Duk da haka, iyalin sun ce har yanzu ba su gamsu ba kuma suna neman a yi cikakken bincike domin gano abin da ya faru tare da tabbatar da adalci.
A martaninsu kan zargin, hukumar gudanarwar Asibitin Kwararru na Jihar Gombe ta musanta zargin, inda ta bayyana shi a matsayin na karya, kuma mara tushe, da bashi da hujja a aikin lafiya.
A cikin wata sanarwa, asibitin ya ce bayanan da ke dakin tiyata sun nuna an yi wa Barira aiki na gaggawa ne kawai, kuma ba a yi mata wani aiki da ya shafi kodarta ba.
Hukumar ta ce bayan da aka shigar da korafin sun gudanar da binciken cikin gida, kuma sun gana sau biyu da Barira da ‘yan uwanta domin bayyana musu sakamakon binciken da kuma duba takardun bayanan likitoci da ke hannunsu.
Asibitin ya kara da cewa daga bisani iyalin sun nemi a sake yi mata wani bincike na daban, kuma hukumar ta amince da hakan kuma ana jiran sakamakon.
Hukumar ta kuma bayyana damuwa kan yadda ake kokarin batawa asibitin suna a kafafen sada zumunta da kuma raunata amincewar jama’a ga ma’aikatan lafiya.
Asibitin ya jaddada cewa ba a cire mata koda ba yayin aikin, kuma yana shirye ya ba da hadin kai ga duk wani bincike na doka.















































