Shugaban Kasa Bola Tinubu a ranar Asabar ya kaddamar da aikin gyara hanyoyin Bama zuwa Banki da Dikwa zuwa Gamboru zuwa Ngala a Jihar Borno da za su kai Naira Biliyan 137.
A lokacin bikin, ya ce idan an kammala hanyoyin, za su inganta kasuwanci, ayyukan noma, da kuma saukaka ayyukan samar da tsaro.
Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN), ya ruwaito cewa za a yi aikin ne a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, a Jihar Borno da ke da iyaka da Jamhuriyar Kamaru.
A yanzu hanyar ta kasance mai hannu biyu, wadda ke da tsawon kilomita 49.15 da fara daga garin Bama a kan iyakar Kamaru.
Tinubu, wanda Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya wakilta, ya ce hanyoyin Bama zuwa Banki da Dikwa zuwa Gamboru zuwa Ngala suna da muhimmanci wajen dawo da harkokin kasuwancin sahara tsakanin Najeriya da kasashen makwabta na Chadi da Kamaru, wadanda ‘yan ta’adda suka lalata.
“Lalatattun hanyoyin, sun kuma kasance masu hadari ne ga tsaro, wurin da yake mai wahala ga jama’a su wuce, suma jami’an tsaro yana basu wahala wajen sintiri da kariya.
Ma’ana alkawura na tabbata ne idan ‘yan kasa za su iya tafiya a kan hanyoyi, su yi jigilar kayansu, su isa ga iyalansu, kuma su zauna cikin tsaro,” in ji shi.
A baya, Alhaji Aliko Dangote, Shugaban rukunin kamfanin Dangote da kwangilar da ke aiwatar da ayyukan, ya ce kungiyarsa tana da manyan hanyoyi 12 wadanda tsawonsu ya wuce kilomita 1,000 a cikin yankuna shida na kasar.
Dangote ya ce ayyukan baki daya sun kai kimanin Naira trillion 3 ga Gwamnatin Tarayya a karkashin Tsarin Biyan Harajin Gina Hanyoyi na Gwamnatin Tarayya.
Ya ce hanyoyin Bama zuwa Banki da Dikwa zuwa Gamboru zuwa Ngala za su bude tattalin arzikin Najeriya, su saukaka ayyukan sojoji, ta haka za su inganta tsaro da jawo masu zuba jari.
A jawabinsa, Ministan Ayyuka, Mista David Umahi, ya ce an fara ba da ayyukan kwangila ne a 2021 akan kusan Naira biliyan 55 amma aikin na samun jinkiri saboda kalubalen rashin tsaro.
Umahi ya ce daga baya aka sake duba kudaden ayyukan, inda aka kiyasta mataki na 1 na Bama zuwa Banki Naira biliyan 70, yayin da mataki na 2 na Dikwa zuwa Gamboru zuwa Ngala ya kai Naira biliyan 67.
A nasa jawabin, Gwamna Babagana Zulum na Borno ya ce wadannan ayyuka suna da matukar muhimmanci a kokarin dawo da jihar yadda take a baya, yana mai cewa hanyoyin za su fadada ayyukan tattalin arziki zuwa Chadi, Kamaru, da Jamhuriyar Nijar. (NAN)













































