Gwamnatin Kano ta rufe makarantun horar da ma’aikatan lafiya biyu saboda gaza cika sharuda

Abba Kabir Yusuf 750x430

Gwamnatin Jihar Kano ta rufe makarantun horar da ma’aikatan lafiya masu zaman kansu guda biyu da ke aiki ba bisa ka’ida ba a Karamar Hukumar Nasarawa saboda kasa cika sharudan doka da ka’idojin ilimi.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa, Jami’in Hulda da Jama’a na Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano, ya sanya wa hannu kuma aka raba wa manema labarai ranar Talata.

SolaceBase ta ruwaito cewa makarantun da abin ya shafa su ne, IBN SINA College of Health Science and Technology da ke Dakata Kawaji kusa da Masallacin Juma’a da kuma Life Line College of Health Science and Technology, wadda ke yankin masana’antu na Dakata, a kan titin Bela, Tsamiyar Gare titin Mai Sikeli.

IMG 20260623 WA0116 IMG 20260623 WA0112

A cewar sanarwar, an rufe su ne bayan cikakken bincike da Ma’aikatar Lafiya ta gudanar, wanda ya gano cewa makarantun biyu ba su cika sharudan da ake bukata da ma’aunai da aka tanadar don kafawa da gudanar da cmakarantun horar da ma’aikatan lafiya a Jihar Kano ba.

Ma’aikatar ta bayyana cewa makarantun suna aiki ne ba tare da tantancewa da amincewar ma’aikatar ba, kuma ba su da takardar shedar amincewa daga hukumomin da suka dace masu kula da ilimi da horar da ma’aikatan lafiya a Najeriya.

Bincike ya nuna, kamar yadda sanarwar ta bayyana, akwai gazawa mai yawa ciki har da rashin isassun malamai kwararru, rashin ingantattun kayan koyo, karancin kayan aiki da gine-gine da kuma gaza bin ka’idojin ilimi da na gudanarwa da ake bukata don horar da ma’aikatan lafiya yadda ya kamata.

Da yake magana kan lamarin, Kofar Na’isa ya ce ma’aikatar na cigaba da himmawa wajen kare dalibai, iyaye da jama’a baki daya daga makarantun da ke lalata ingancin ilimi da ma’aunan kwarewa.

“Horon ma’aikatan lafiya dole ne a gudanar da shi a cibiyoyin da suka cika ka’idoji da bukatun doka kadai,” in ji shi.

Ya kara da cewa gwamnati za ta cigaba da tabbatar da bin dokokin da ke jagorantar makarantun horar da ma’aikatan lafiya a fadin jihar domin kare martabar ilimin kiwon lafiya da kwarewa.

Gwamnatin Jihar Kano ta kuma gargadi masu makarantun horar da ma’aikatan lafiya a fadin jihar da su bi dukkan dokoki da tanade-tanaden da ke jagorantar ayyukansu.

A cewar ma’aikatar, rufe cibiyoyin da ba su bi ka’ida ba ya zama wajibi domin tabbatar da ingancin ilimin kiwon lafiya, tabbatar muradun dalibai da tabbatar da ayyukan kiwon lafiya a fadain Jihar Kano.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here