Gwamnatin Kano ta karyata barkewar cutar kyanda

Cutar, Kyanda, gwamnati, kano
Gwamnatin jihar Kano a Najeriya ta yi amai ta lashe game da barkewar cutar kyanda a karamar hukumar birni. A ranar Lahadin da ta gabata ne jami’an lafiya na...

Gwamnatin jihar Kano a Najeriya ta yi amai ta lashe game da barkewar cutar kyanda a karamar hukumar birni.

A ranar Lahadin da ta gabata ne jami’an lafiya na karamar hukumar birnin suka tabbatar da barkewar cutar a wasu unguwannin karamar hukumar.

A wata sanarwa da aka rabawa manema labarai karkashin ma’aikatar lafiya ta jihar mai dauke da sa hannun Daraktan kula da cututtuka masu yaduwa Dakta Imam Wada Bello ta ce labarin barkewar cutar karyace zalla.

Karin labari: Sudan ta amince shigar da agaji ta ƙasashe maƙwabta

Dakta Imam ya ce kafin a ayyana cuta a matsayin annoba, akwai wasu matakai da ake bi, kuma jami’an lafiyar karamar hukumar basu bi wadannan ka’idoji ba, kawai suka yi riga malam masallaci wajen ayyana barkewar cutar.

Karin labari: Shugaban jam’iyyar APC Omotoso ya rasu

Darakta Imam ya ce ma’aikatar harkokin lafiya ta jihar Kano na iya bakin kokarin ta wajen sanya idanu kan cututtuka masu yaduwa da kuma hana su barkewa don haka ba hakki ne na jami’an lafiya matakin karamar hukuma su sanar da barkewar cuta ba, hakki ne na ma’aikatar lafiya a mataki na jiha.

Daga nan kuma sai ya bukaci al’ummar jihar su kwantar da hankalin su, babu annobar cutar a dukannin fadin kananan hukumomi 44 na jihar ta Kano.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here