Ɗalibin Nijar ya rasu a hanyar komawa gida daga Sudan

39b7bdc6 c7b3 46f1 bb6e 0d1ed52a08a6
39b7bdc6 c7b3 46f1 bb6e 0d1ed52a08a6

Wani ɗalibi ɗan ƙasar Nijar ya rasu a hanyar komawa gida daga Sudan bayan an kwaso su yayin da ake ci gaba da gwaɓza faɗa tsakanin sojojin gwamnati da kuma dakarun RSF.

Ɗaya daga cikin wakilan ɗaliban, Ahmad Rabe Kani, ya ce ɗalibin ya rasu ne a kan hanya kafin su isa gida.

Ya ce sun bar Sudan cikin ƙoshin lafiya tare da ɗalibin, amma da zuwan su Chadi sai ya yanke jiki ya faɗi.

Ya ce a yanzu an isa Yamai da gawar ɗalibin domin yi masa jana’iza.

Ɗaliban Nijar ɗin dai sun shafe tsawon kwanaki a Port Sudan kafin daga bisani su isa zuwa N’djamena da kuma komawa ƙasarsu ta wani jirgin soji.

Ya ce su ɗaliban sun kai 45, inda ya ce akwai sauran mutum takwas a birnin Port Sudan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here