
Kungiyar marubutan wasanni ta Najeriya SWAN, ta yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta nada kwararru masana harkokin wasanni don gudanar da harkokin kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars FC da sauran sassan wasanni a jihar.
SWAN ta kuma yi kira da a gyara da inganta filin wasa na Sani Abacha da filin wasa na Kano Pillars da kuma Mahaha Sports Complex da Ado Bayero Square, da duk sauran wuraren wasanni na jihar.
Wannan zai samar da yanayi mai kyau ga ‘yan wasa don bunƙasa da kuma ɗaukar nauyin al’amuran ƙasa da na duniya.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi mai dauke da sa hannun Zaharaddeen Sale da Muhammad Nur Tijjani, shugaba da sakataren kungiyar SWAN reshen jihar Kano, bi da bi.
“Wannan yunkuri, muna kyautata zaton zai samar da sakamako mai kyau da kuma daukaka matsayin wasanni a jihar Kano.
“Kungiyar SWAN reshen jihar Kano, ta jajanta wa rigingimun da suka addabi kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars. Mun fahimci kalubalen da kungiyar ke fuskanta kuma muna kira ga masu ruwa da tsaki su hada kai don magance matsalolin.
Karin labari: Farfesa Jibril Diso na farko a Najeriya ya rasu
“Tunaninmu yana tare da ‘yan wasa da masu horarwa, da magoya baya a wannan mawuyacin lokaci. Mun yi imani da juriyar kungiyar da kuma kishin magoya bayanta.
“Muna fatan za a gaggauta warwarewa tare da dawowa Kano Pillars FC nasara.
“Muna yi wa gwamnatin jiha da ma’aikatar kula da matasa da wasanni ta Kano fatan samun nasara a ayyukansu da kuma fatan hada kai da su domin bunkasa harkokin wasanni a jihar Kano” in ji sanarwar.
Idan za’a iya tunawa kasa da makonni ne kwamishinan matasa da wasanni Mustapha Rabi’u Kwankwaso ya rushe shugabancin gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars.