Farfesa Jibril Diso na farko a Najeriya ya rasu

Farfesa, Jibril, Diso,farko, Najeriya, rasu
Farfesa Jibril Isa Diso, Farfesa na farko da yake fama da nakasa a Najeriya ya rasu. Shugaban sashen hulda da jama’a na Jami’ar Bayero Lamara Garba, ya...

Daga: Aliyu Inuwa Mansur

Farfesa Jibril Isa Diso, Farfesa na farko da yake fama da nakasa a Najeriya ya rasu.

Shugaban sashen hulda da jama’a na Jami’ar Bayero Lamara Garba, ya tabbatar da rasuwar sa ga Jaridar Solacebase a ranar Juma’a.

Har zuwa rasuwarsa Jibril malami ne a Sashen Ilimi na Musamman a Jami’ar Bayero ta Kano.

An haife shi a unguwar Diso da ke karamar hukumar Gwale a jihar Kano.

Karin labari: “Ya kamata NFF ta bar Finidi a matsayin Koci” – Shaibu

Jibril ya fara karatunsa ne a shekarar 1962 ya kuma kammala karatunsa na firamare a shekarar 1969.

Ya halarci makarantar sakandaren makafi ta Gindiri da ke jihar Filato a shekarar 1979, daga nan ya ci gaba da karatunsa a makarantar Tudun Maliki ta masu bukata ta musamman da ke Kano kafin ya shiga Sashen ilimi na musamman a Jami’a a shekarar 1994.

Karin labari: Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu ya kammala ganawa da shugabannin kungiyoyin kwadago

A shekarar 2019, ya zama farfesa mai matsalar gani na farko a Najeriya.

Jibril ya samu digirin digirgir a fannin ilimi na musamman a jami’ar Birmingham da ke Landan a shekarar 1991.

Za’ayi Sallar Jana’izarsa a yau da karfe 1:00 na rana a Masallacin Juma’a na Abdullahi Bin Abbas da ke Sabon Titi a Gidan Kankara Jihar Kano.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here