Abba Kyari ya musanta mallakar kadarorin da hukumar NDLEA ta danganta da shi a shari’ar zargin kin bayyana kadarori

Abba Kyari2

Tsohon mataimakin kwamishinan ’yan sanda da aka dakatar, Abba Kyari, ya musanta mallakar wasu kadarori da hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ta danganta su da shi a shari’ar da ake yi masa bisa zargin kin bayyana kadarorinsa.

Kyari ya bayyana hakan ne a gaban mai shari’a James Omotosho na babbar kotun tarayya da ke Abuja, lokacin da ya fara kare kansa a matsayin wanda ake ƙara na farko. Ya ce wasu daga cikin kadarorin da ake zargi da mallakarsu na mahaifinsa marigayi ne, wanda ya bar yara kimanin 30.

Ya ce takardun kadarorin suna hannun ma’aikatar ƙasa ta jihar Borno, tare da ƙaryata zargin cewa shi ne mai filin wasan polo a jihar.

Ya ce filin polo ya dade tun yana yaro, kuma bai taɓa mallaka ko gina wani abu a wurin ba.

Sai dai Kyari ya amince da mallakar wani filin noma da ke kan titin Abuja zuwa Kaduna, wanda ya ce yana noma a wurin sama da shekaru goma.

Haka kuma, ya tabbatar da cewa yana da asusun ajiya a bankunan UBA, Access da GTB, inda ya bayyana cewa fam dubu bakwai da aka samu a asusun waje nasa an bayyana su bisa ƙa’ida kafin wannan lokaci.

Ya ƙara da cewa asusun ajiyarsa an kulle su sakamakon shari’ar, yayin da ya ce bai taɓa halartar kama masu safarar miyagun ƙwayoyi a filin jirgin sama na Enugu ba, saboda jami’an NDLEA ne suka aikata abin da ake tuhuma.

Ya kuma ce, ya miƙa kansa ga bincike ne ta ofishinsa bayan zargin ya fito fili.

Kotun ta dage cigaba da sauraron shari’ar zuwa 5 ga watan Nuwamba.

A baya, mai shari’a Omotosho ya ƙi karɓar bukatar Kyari da ’yan uwansa biyu na neman kotu ta watsar da karar, inda ya ce akwai hujjojin da suka isa don a saurari kare kansu. Hukumar NDLEA ta tuhume su da kin bayyana kadarori da kuma ɓoye asalin mallaka, wanda ya sabawa sashe na 35(3)(a) na dokar NDLEA da sashe na 15(3)(a) na dokar hana halatta kuɗaɗen haram.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here