Gwamnan Kano ya yaba da ƙoƙarin sojoji wajen yaƙi da ‘yan bindiga

WhatsApp Image 2025 11 05 at 06.14.36 750x430

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya jinjinawa rundunar sojojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro bisa saurin daukar mataki kan hare-haren ‘yan bindiga da suka faru a wasu sassan jihar.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature, ya fitar a Kano a ranar Laraba, gwamnan ya bayyana godiyarsa ga dakarun sojoji saboda jajircewarsu da kuma sadaukarwar da suke nunawa wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Yusuf ya yi wannan yabo ne lokacin da babban kwamandan rundunar sojoji ta 1 da ke Kaduna, Manjo Janar Abubakar Wase, ya kai masa ziyarar ban girma a gidan gwamnatin Kano.

Gwamnan ya gode wa shugaban ƙasa Bola Tinubu bisa nada hafsoshin tsaro masu ƙwarewa da kishin ƙasa waɗanda ke jajircewa wajen tabbatar da tsaro a fadin ƙasar.

Haka kuma, Yusuf ya sanar da bayar da tallafin motocin Hilux guda 10 da babura 60 ga dakarun hadin gwiwa da ke gudanar da ayyukan tsaro a yankunan da matsalar ta shafa.

Ya tabbatar da kudirin gwamnatinsa na ci gaba da tallafawa hukumomin tsaro domin yaƙi da ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane, da masu satar shanu a jihar Kano.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here