‘Yan uwan daliba a Kano na neman adalci kan mutuwarta bayan zargin hukunci mai tsauri a makaranta

Kano Map (1)

Damuwa da bakin ciki sun lullube iyalin wata yarinya mai shekaru 14, Maimuna Sani Yaro, wadda ake yi wa lakabi Nihal, wadda mutuwarta ta haifar da damuwa da kiran neman adalci a Jihar Kano.

Nihal, wata daliba a aji 2 na karamar Makarantar Sakandare (JSS 2) a St. Louis da ke Kano, an ruwaito ta rasu ne bayan ta sha azaba a makaranta, lamarin da ya haifar da damuwa sosai a tsakanin iyaye, masu ruwa da tsaki a fannin ilimi da masu kare hakin kananan yara.

Mahaifiyar Nusaiba Danshareef, tana cikin matsananciyar damuwa rasa ’yarta tilo.

Da take zantawa da tashar Arewa Radio cikin kuka, ta zargi hukumomin makaranta da kokarin boye abin da ya faru da yarinyar.

A cewar Danshareef ta ce an fara yin tambayoyi kan abin da ya faru na gaskiya bayan da makarantar ta sanar da ‘yan uwa cewa Nihal ta fado ta mutu.

Zargin ya kara karuwa kamar yadda ta ce, lokacin da Mataimakiyar Shugabar Makarantar, Halima Babayaro, ta ziyarce su domin yi musu ta’aziyya.

“Ta roke ni in da na manta da duk wata magana da za a yi nan gaba kan dalilin mutuwar ’yata,” Danshareef ta bayyana. “Wannan magana ce ta sa na fara tunanin akwai wani abu sama da abin da muka ji.”

Ta ce washegari, wayarta ta cika da hotunan rubutu da sakonnin dalibai da ke dauke da tambarin #JusticeForNihal. A fahimtarta, yakin neman adalcin na kan layi ya nuna cewa daliban sun yi imani akwai tambayoyi da ba a amsa ba kan mutuwar.

“Wannan ya kara tabbatar min da shakkuna cewa akwai zamba da kokarin boye abin da ya faru na gaske,” in ji ta.

Yayin da iyali ke neman amsa, an ce sabbin bayanai sun fara bayyana. Wasu daliban da suka san Nihal sun ce an yi mata hukunci mai tsauri wanda ya bukaci ta tsaya a cikin zafin rana na sa’o’i da dama.

Bisa ga abin da iyalin suka ji, Nihal ta fadi daga baya aka garzaya da ita asibiti a Kano, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarta.

Zarge-zargen sun haifar da tambayoyi masu yawa kan tsarin hukunci a makarantu, sannan kuma azabar idan ta tabbata, ta yi daidai lafiya ga karamar daliba.

Lamarin ya sake haifar da muhawara a fili kan duka da sauran hanyoyin horar da dalibai, musamman a lokacin da masu kare hakin kananan yara ke kira ga yin amfani da hanyoyi masu mutunta dan adam.

Duk da cewa ana ci gaba da nuna damuwa, makarantar ba ta fitar da wata sanarwa ba tukuna domin yin Magana kan zarge-zargen ko bayyana abin da ya faru kafin mutuwar dalibar.

Duk da haka, Sakatare Zartarwa na Hukumar Makarantu masu zaman kansu ta Jihar Kano, Baba Umar, ya bayyana cewa tawagar da aka tura don gano hakikanin lamarin, ta sanar da su cewa Limamin makaranta ne ya hukunta Nihal kan zargin rashin zuwa masallaci a kan lokaci.

A Danshareef da iyalinta, zafin rasa yarinyar ya ci gaba da zama abu mai sosa rai. Amma bayan bakin cikin, akwai kuduri na neman amsa da daukar alhaki.

Yayin da bincike ke gudana, mazauna Kano da dama na kallo, suna fatan gaskiyar da ta dabaibaye mutuwar Nihal za ta bayyana kuma darussan da za a koya daga wannan bala’i zai taimaka wajen hana maimaita irin wannan lamarin a nan gaba.

A halin yanzu, sakonnin #JusticeForNihal na ci gaba da yaduwa, yana zama hanyar yin kira da wadanda ke neman bayani, daukar alhaki da adalci ga karamar yarinyar da aka yankewa rayuwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here