Hukumar kiyaye aukuwar hadura ta Kasa tace kamfanin kera motoci na Toyota da ke kasar China ya dawo da motoci kirar Lexus guda Dubu 14 da 799 da suka lalace.
Mai magana da yawun hukumar Kuma Jami’in kula da sashen wayar kan jama’a Bisi Kazeem, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Abuja.
Kazeem ya ce “hukumar ta FRSC na fatan jawo hankalin jama’a masu tuka mota, musamman wadanda ke amfani da motocin Kira Lexus NX260 da Lexus NX3650h da kuma Lexus NX400h+, wanda aka kera tsakanin 31 ga watan Maris, din 2021, da 26 ga Afrilun 2022.
“A cewar wani rahoto da ke kunshe a cikin wata takarda da ofishin sakataren gwamnatin tarayya ya aikewa, kamfanin na Lexus.
Kazeem ya ce, an ja hankalin al’umma ne musamman kan cewa motocin za su iya haddasa hadura ga masu amfani da su.
Inda ya hakaito, mukaddashin shugaban rundunar, Dauda Biu, na gargadin jama’a musamman dillalai da direbobin wadannan nau’ukan motoci da su daina siyar da su.
Biu ya kuma ja kunnen jama’a da su daina yin amfani da nau’ikan motocin a kan titunan Najeriya domin gujewa duk wata matsala.












































