Dalilan dasuka janyo na yi murabus daga Kwamitin yakin neman zaben APC a Adamawa – Sen. Binani.

en. Aishatu Binani
en. Aishatu Binani

Jam’iyyar APC reshen jihar Adamawa ta tabbatar da murabus din Sen. Aishatu Binani a matsayin wakiliya a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC a Adamawa.

Sakataren Jam’iyyar Mista Raymond Chidama ya tabbatar da hakan yayin da yake zantawa da manema labarai bayan taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a Yola.

Ya ce murabus din nata ya biyo bayan soke zaben fidda gwani da ya kaita matsayin ‘yar takarar gwamna a jam’iyyar da babbar kotun tarayya Yola ta yi.

Da take zantawa da manema labarai, Aisha Binani ta danganta murabus din nata da wata shari’ar daukaka kara datake yi, wanda ta ce tana bukatar samun kulawar ta, kuma da alama hakan zai yi tasiri a yakin neman zaben Mista Tinubu da ke gudana a fadin kasar.

“Na sauka ne domin baiwa wani damar yin aiki a madadina har zuwa lokacin da za a yanke hukunci akan karar da nake yi, in ji ta.

Chindama ya ce, Babale Martins, mataimakin gwamna ga tsohon Gwamna Muhammad Bindow, shi ne zai cigaba da jagorancin kwamitin yakin neman zaben a jihar.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa, wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Yola a ranar 14 ga watan Oktoba ta soke zaben fidda gwanin gwamnan Adamawa na jam’iyyar APC wanda ya samar da Sen. Aishatu Binani a matsayin ‘yar takarar gwamna a jam’iyyar a 2023.

A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Abdulaaziz Anka ya ce jam’iyyar APC ba ta da dan takarar gwamna a zaben 2023 a jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here