Wata kungiyar rajin tabbatar da adalci da daidaito ga ‘yan kasa mai suna Citizens Stability Forum ta soki tsarin da kasar Amurka da Birtaniya suka dauka kan batun tsaro da aka yi a Najeriya.
Jaridar Solacebase ta ba da labarin cewa ƙasashen sun bada shawarwarin takaita zirga-zirga da tafiye-tafiye ga mutanen su, sannan kuma da wasu ofisoshin jakadancin kasashen waje a Najeriya.
Kasashen sun gargadi ‘yan kasar da su guji yin balaguro zuwa Najeriya, musamman Abuja, tare da gargadin yiwuwar kai harin ta’addanci a birnin.
Da yake jawabi ga manema labarai a Kano a ranar Juma’a, jagoran kungiyar Mukhtar Lawal, ya ce faɗakarwar game da tsaro ta haifar da firgici da fargaba a tsakanin ‘yan Nijeriya, lamarin da ya bayyana a matsayin abin takaici.
Muktar ya ce kamata ya yi kasashen Amurka da Birtaniya su zauna a sirrance da gwamnatin Najeriya ta hanyar diflomasiyya tare da hada hannu da jami’an tsaro na kasar don dakile barazanar da ake tunanin ka iya faruwa maimakon tayar da hankali.
“Wannan matakin na faɗakarwar tsaro da Amurka, Birtaniya da sauran ƙasashen waje suka yi ya haifar da fargabar da ba a taɓa gani ba a rayuwar ‘yan Najeriya musamman mazauna Abuja kuma hakan zai iya raunana mutuncin jami’an tsaron mu.”
Kungiyar ta bukaci gwamnatin tarayya da ta ja hankalin gwamnatocin Amurka da na Birtaniya kan bukatar su mutunta ka’idojin tsaron kasa da kasa dan gudun tashin hankali.
Yayin da hakan yayi matukar tasiri, ya zama wajibi ‘yan Najeriya da gwamnatin Najeriya su ja hankalin gwamnatin Amurka kan bukatar mutunta ka’idojin tsaro kan musayar bayanan sirri a kasar nan.
Ya kamata a tunatar da Amurka cewa irin wannan matakin na bainar jama’a na ofishin jakadancin Amurka baya ga kin mutunta ka’idar musayar bayanan sirri na tsaro da gwamnatin Najeriya zai kara sanya karfin gwiwa ga ‘yan ta’adda da kuma tabarbare rayuwar ‘yan kasa da mazauna kasar.













































