Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP Dr Rabi’u Musa Kwankwaso ya shawarci duk wadanda suka cancanci kada kuri’a a kasar nan da su samu lokaci dan karanta kundin manufofin sa na tabbatar da shugabanci nagari.
Kwankwaso ya bayyana hakane jim kadan bayan kammala Sallar Juma’a na raka’a biyu a Masallacin Al-Habibiyah Islamic Society.
Tsohon gwamnan Kano da ya yi wa’adi biyu ya ce akasarin abin da ya yi niyyar yi idan aka zabe shi a matsayin shugaban Najeriya a 2023 na kunshe cikin kundin manufofin.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya rawaito cewa Kwankwaso, a cikin takardarsa mai shafuka 160 da manufofinsa mai suna “Alkawurra na zuwa gare ku: ya bayyana alkawura 20 da zai cika idan aka zabe shi.
“Za mu yi adalci ga kowa kuma za mu tabbatar da gaskiya da adalci a kowane mataki na mulki,” in ji Kwankwaso.
A nasa bangaren, babban limamin masallacin Al-Habibiyyah, Dr Fuad Adeyemi ya yi kira ga daukacin al’ummar Musulmi da su yi aiki tukuru domin kasar nan ta samu daidaito daga wannan hali da take ciki.
A cewarsa, idan dukkan musulmi suka yanke shawarar yin abin da ya dace da taimakon juna, hakan zai kawo zaman lafiya a kasar.
“Tsoron Allah ya kamata ya zama jagorar mu ba abin da za mu amfana ba,” in ji Adeyemi.













































