Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta karyata wata sanarwar manema labarai da aka fitar dangane da batun matsayar siyasar tsohon dan takararta na shugaban kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, na komawa jam’iyyar APC mai mulki a shekarar 2027.
Sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa, Ladipo Johnson, a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Abuja, a ranar Asabar, ya bayyana cewa sanarwar, ba ta taba fitowa daga shugaban jam’iyyar NNPP na kasa,’ Sanata Musa Kwankwaso ba, don haka ya bukaci jama’a da su yi watsi da ita a matsayin aikin masu yin barna.
Sanarwar, a cewar Johnson, ta bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Kano ya ki amincewa da rokon da shugaba Bola Tinubu ya yi masa kan komawar Kwankwaso jam’iyyar APC ne bisa la’akari da ra’ayinsa da kuma son da yake yi na siyasa har ma da sukar manufofin gwamnatin tarayya da tasirinsa ga jama’a.
Johnson ya ci gaba da cewa, da gangan Kwankwaso ya kauracewa yin tsokaci kan al’amuran siyasa na zamani kuma zai ci gaba da yin hakan a halin yanzu.
Jam’iyyar ta bukaci jama’a da su rika amfani da sahihan bayanai da suka fito daga hannun Kwankwaso da sauran manyan kafofin jam’iyyar, maimakon irin wadannan labaran karya da ake yadawa a kafafen yada labarai da nufin yaudarar jama’a.













































