Gwamnan Kano ya dakatar da mataimakinsa saboda wata sanarwa da ya fitar ba da izini ba

Abba Kabir Yusuf Kano Kano 715x430

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin dakatar da babban mai ba da rahoto na musamman (SSR) Ibrahim Rabi’u da ke ma’aikatar sufuri bisa wasu kalamai da ya fitar ba da izini ba.

Baya ga haka, gwamnati ta bayar da umarnin a gabatar da tuhuma ga wanda aka dakatar saboda kalaman da ya yi na tada zaune tsaye a kan zargin sauya sheka da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi.

SolaceBase ta tuna cewa Ibrahim Rabi’u, a ranar Asabar, ya fitar da wata sanarwa da aka ce yana bayyana matsayar Kwankwaso a kan jita-jitar komawarsa APC.

An kuma ce, sanarwar da mai taimaka wa gwamnan ya fitar, ta fito daga hannun Kwankwaso da NNPP.

Sakataren gwamnatin jihar Alhaji Umar Farouk Ibrahim ne ya bayar da sanarwar dakatarwar SSR ɗin wadda ta fara aiki nan take a ranar Asabar.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, gwamnatin ta gargadi duk masu rike da mukaman siyasa kan su guji yin kalaman da ba su da tabbas, inda ta nace cewa duk wani bayani a hukumance dole ne ya samu izini.

Don haka gwamnati ta tunatar da jama’a cewa Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim Waiya ne kadai ke da ikon yin magana a madadin gwamnati yayin da babban daraktan yada labarai Sanusi Bature ke magana a madadin Gwamna.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here