Gwamnatin Kano da masu ruwa da tsaki sun kaddamar da matakan magance karin farashin Biredi

Bread 727x430

Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da wani kwamiti da zai magance tashin farashin biredi a jihar, biyo bayan nuna damuwa da mazauna jihar ke yi kan tsadarsa.

Da yake jawabi yayin wani taron da aka gudanar a ranar Asabar, kwamishinan kasuwanci, saka hannun jari da masana’antu, Shehu Wada Sagagi, ya ce matakin ya biyo bayan umarnin da gwamnan jihar ya bayar a matsayin martani ga koke-koken da jama’a suke yi kan tsadar biredi.

“Kwanaki da suka gabata, Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, ya umarce ni da in zauna da kungiyar masu Buredi da kungiyar kare kasuwa da cigaban kasuwar Singa, domin nemo hanyoyin yin biredi da sauki,” in ji Kwamishinan.

A cewarsa, bayan tattaunawa da gwamnati da masu ruwa da tsaki, sun amince da kafa wani kwamiti da zai duba wasu muhimman batutuwa.

Wadannan sun hada da tantance adadin gidajen biredi da ke aiki a jihar, ba da shawarar hanyoyin daidaita biredi da masu yin burodi ke amfani da su, da kuma binciko matakan rage farashin biredi.

SolaceBase ta ruwaito cewa, kwamitin zai kuma duba kalubalen da ke fuskantar sana’ar biredi a Kano, da tantance yanayin tsafta da tsaftar gidajen biredi, tare da tabbatar da cewa gidajen biredi sun cika ka’idojin da aka tsara.

Sakataren kungiyar masu yin burodi a Kano, Ado Suleiman, shi ne ya zama shugaban kwamitin, yayin da sauran mambobin kwamitin sun hada da Nura Ibrahim, Kabiru Adamu, Usman Sadiq, Barista Junaidu Muhammad Zakari, da Abubakar Kibiya, babban mataimaki na musamman kan bunkasa tattalin arzikin gwamna, wanda zai zama sakatare.

Sagagi ya tabbatar da cewa gwamnati ta himmatu wajen ganin gidajen biredi sun bunkasa tare da daukar nauyin masu sana’ar. Ya kara da cewa “Gwamnatin jihar za ta dauki kwakkwaran mataki kan wadanda ke damfara a harkar samar da kayayyaki.”

Shugaban kungiyar masu yin burodi, Alhaji Jibrin Abubakar Garba, ya yaba da yadda gwamnati ta shiga tsakani, inda ya bayyana cewa rashin daidaita hanyoyin samar da abinci ya haifar da matsalar farashin da ake samu a yanzu.

Shima da yake nasa jawabin shugaban kungiyar raya kasuwar Singa Barista Junaidu Muhammad Zakari yace farashin fulawa ya fara daidaita har ma ya ragu.

Ya bayyana fatansa cewa sabon kwamitin da aka kafa zai yi aiki tukuru domin cimma burinsa da kuma kawo sauki ga masu amfani da su a fadin jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here