Gwamnatin jihar Kano ta bayyana matukar damuwarta dangane da ibtila’in gobara da ta lakume gonaki da Rumbuna da kuma dabbobi a yankin Zago da ke karamar hukumar Dambatta.
Gwamnatin ta kuma yi alkawarin tallafa wa wadanda abin ya shafa da kudade domin rage musu hasara da kuma taimaka musu wajen farfado da barnar da gobarar ta haddasa.
Kwamishinan kasuwanci, zuba jari da masana’antu, Alhaji Shehu Wada Sagagi, wanda ya ziyarci al’ummar a madadin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya bayyana hakan a ranar Juma’a.
Karin karatu: Zamfara: Dalibai 17 sun mutu sakamakon tashin gobara
Sagagi ya jajanta wa wadanda abin ya shafa tare da tabbatar musu da cewa gwamnati za ta tantance asarar da aka yi tare da bayar da diyya domin rage musu radadin da suke ciki.
Tawagar da ta kunshi jami’an hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar (SEMA) da hukumar ba da agajin gaggawa ta Kasa (NEMA) sun yi kira ga al’ummar yankin da su tantance barnar da gobarar ta yi tare da hada rahoto.
SolaceBase ta ruwaito cewa gobarar ta tashi ne da safiyar Laraba da misalin karfe 10:30 na safe, inda ta lalata gonaki, da kayan abinci na miliyoyin naira, tare da kashe tumaki da awaki sama da 40.
Shedun gani da ido sun ce gobarar ta kuma lalata rumbun ajiyar hatsi sama da 20, gidaje biyu, da shanu akalla biyu.
Ibtila’in ya jefa mazauna yankin cikin kunci, musamman ganin yadda azumin watan Ramadan ke gabatowa, kuma rumbunan abincin su sun ƙone.