Shugaban hukumar kula da aikin Hajji na kasa (NAHCON) Farfesa Saleh Usman, ya sanar da tsawaita wa’adin rajistar aikin Hajjin 2025 zuwa ranar 10 ga Fabrairun 2025.
A cewar wata sanarwa mai dauke da sa hannun mataimakiyar daraktar yada labarai ta NAHCON, Fatima Sanda Usara tace, matakin ya biyo bayan roko da aka yi a madadin maniyyatan da suka kasa kammala rajistar su kafin wa’adin da aka bayar tun ranar 31 ga watan Janairun 2025.
A yayin da yake sanar da tsawaita wa’adin a taron da suka gabatar a Zoom tsakanin NAHCON da masu ruwa da tsaki a aikin Hajji a daren ranar Talata, shugaban ya bukaci sakatarorin zartaswa na hukumar jin dadin alhazai na jihohi da su baiwa hukumar hadin kai domin ganin sun mika kudaden a kan lokaci, inda ya ce kudaden na da matukar muhimmanci wajen samun masauki a kan kari.
Labari mai alaƙa: NAHCON ta nemi CBN ta cire kashi 2% na kudaden Alhazai
“Yana da mahimmanci a lura cewa Saudiyya ta sanya ranar 14 ga Fabrairu, 2025, a matsayin wa’adin da aka kulla yarjejeniya, wannan yana nufin duk abin da za a biya dole ne ya isa ga asusun da aka keɓe a Saudi Arabia kafin wannan ranar don tantance shi”.
Usara ta kuma bayyana cewa, masu ruwa da tsaki sun amince da gudanar da tarukan tattauna batutuwa aikin hajjin ta Zoom akai-akai har sai an kammala dukkan shirye-shirye.
A cewar sanarwar, wani muhimmin batu da aka tattauna a kai shi ne shawarar da babban bankin kasar CBN ya bayar na bayar da alawus-alawus din tafiye-tafiye ta hanyar katin kiredit, wanda da yawa daga cikin mahalarta taron suka nuna adawa da irin wahalar da zai iya haifar wa alhazai.