Kotun koli ta tabbatar da Mutfwang a matsayin gwamnan jihar Filato

Plateau State Governor Caleb Mutfwang
Plateau State Governor Caleb Mutfwang

Kotun kolin kasar nan ta tabbatar da Caleb Mutfwang a matsayin zababben gwamnan jihar Filato.

Kutun ta amince da daukaka karar da Mutfwang ya shigar, na neman a maido masa da kujrar gwamnan Jihar, bayan da ta janye hukuncin da kotun daukaka kara ta yi.

Mai shari’a Emmanuel Agim wanda ya yanke hukuncin ya ce daukaka karar da gwamnan ya yi shi ne abin da ya dace.

Karanta wannan: Kotun Koli ta tabbatar da Bala Muhammad a matsayin gwamnan jihar Bauchi

Kamfanin dillancin Labarai NAN ya rawaito cewa a watan Nuwamba ne kotun daukaka kara ta yanke hukuncin cewa Muftwang ba jam’iyyarsa ta PDP ce ta ci zaben ba.

Kotun ta ce Nentawe Yilwada na jam’iyyar APC ne ya lashe zaben don haka ne ya daukaka karar.

Karanta wannan: Yanzu-yanzu Kotun koli tabtabbatarwa da Abba gida-gida nasara

Sakamakon da hukumar INEC ta bayyana, a baya ya nuna cewa Mutfwang ya samu kuri’u 525,299 inda ya yi nasara akan Yilwada wanda ya samu kuri’u 481,370.

Tun da farko kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Filato ta tabbatar da nasarar Muftwang wanda ya sa Yilwada ya shigar da kara a kotun daukaka kara.

Hukuncin da kotun koli ta yanke kan shari’ar shi ne ya zama na karshe.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here