Kotun kolin kasar nan ta tabbatar da Dauda Lawal na jam’iyyar PDP a matsayin gwamnan jihar Zamfara.
Kotun kolin ta yi watsi da hukuncin da kotun daukaka kara ta Abuja ta yanke a baya, inda ta bayyana zaben gwamna a matsayin wanda bai kammala ba, sannan ta bayar da umarnin sake zabe a kananan hukumomi uku na jihar.
Karanta wannan: Kotun koli ta tabbatar da Mutfwang a matsayin gwamnan jihar Filato
A watan Nuwamba ne kotun daukaka kara ta soke zaben Lawal.
Ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan da aka yi ranar 18 ga watan Maris, da wani gagarumar tazara tsakaninsa da Bello Matawalle na jam’iyyar APC a lokacin.
Ya samu kuri’u 377,726 yayin da Bello Muhammad Matawalle kuma ya samu kuri’u 311,976.
Karanta wannan: Kotun Koli ta tabbatar da Bala Muhammad a matsayin gwamnan jihar Bauchi
Dan takarar na jam’iyyar APC, wanda a yanzu yake rike da mukamin karamin ministan tsaro, ya zargi hukumar INEC da murda nasarar da ya samu a zaben, ta hanyar kin sanya sakamakon wasu akwatuna.
A wani hukunci da ta yanke a baya a ranar 18 ga watan Satumba, kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar Zamfara ta tabbatar da nasarar Lawal.