Tinubu ya nada Ali Nuhu da wasu mutane 10 a matsayin shugabannin hukumomi

President Bola Tinubu signs
President Bola Tinubu signs

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya nada jarumin fina-finan Nollywood, Ali Nuhu, da wasu mutum 10 a matsayin sabbin shugabannin hukumomin da ke karkashin ma’aikatar raya al’adu ta tarayya.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya fitar ranar Juma’a a Abuja.

Ya ce Tinubu ya bukaci sabbin wadanda aka nada da su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu ta hanyar da ya dace tare da nuna kwarewa, kwazo da kishin kasa.

Wadanda aka nada sun hada da Ali Nuhu da Tola Akerele, da kuma Dakta Shaibu Hussain.

Sauran sune Obi Asika da Aisha Adamu Augie da Ekpolador-Ebi Koinyan da Ahmed Sodangi da Chaliya Shagaya da Hajiya Khaltume Bulama Gana, sai Otunba Biodun Ajiboye da Ramatu Abonbo Mohammed.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here