Kungiyar Burnley ta dauki Fofana aro daga Chelsea

Fofana
Fofana

Burnley ta dauki dan wasan Ivory Coast David Dtro Fofana daga Chelsea a matsayin aro zuwa ƙarshen kakar wasanni.

A watan Janairun 2023 nan ne Fofana ya koma Stamford Bridge kan kwantaragin shekara shida daga ƙungiyar Molde ta Norway.

Karanta wannan: Dan wasan kwallon kafa ya yanke jiki ya fadi, ya mutu

Rabin kakar da aka fara ya kare ta ne a matsayin aro a ƙungiyar Union Berlin da ke Jamus, inda ya buga mata wasa 17, kuma ya ci mata kwallo a wasan da ta yi a Champions da Napoli.

Ana ganin matashin ɗan wasan mai shekara 21 zai yi daidai da ƙungiyar domin ci gabansa.

Karanta wannan: Manchester City Ta Yiwa Real Madrid Raga-Raga A Wasan Kusa Da Na Karshe

Dan wasan zai iya buga Premier da FA cikin sharaɗin da aka sanya yayin bayar da shi aro.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here