Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta lashe gasar cin kofin shugaban shugaban kasa Muhammadu Buhari mai taken ‘Presidential Cup’.
Mai bawa Shugaban kasa shawara kan harkokin wasanni wanda tsohon dan wasan Super Eagles ne Daniel Amokachi shine ya shirya gasar, a wani bangare na wasannin share fagen shiga gasar Firimiyar shekarar 2021/22.
An gudanar da gasar daga ranar 10 zuwa 12 ga Disamba 2021, a filin wasa na MKO Abiola dake birnin tarayya Abuja, da ƙungiyoyi Hudu suka fafata a kofin.
Daga cikin ƙungiyoyin sun hada da zakaran gasar Kano Pillars sai Sunshine Stars da Akwa United sai kuma Lobi Stars.
Pillars ta samu galaba a wasanni biyu data doke Sunshine Stars daci 3-1 , sai Lobi Stars da ci 2-1 , ta kuma yi Canjaras da Akwa United da 1-1, da hakan ya sa ta kammala gasar da maki 7, sai Sunshine ta kare a na biyu da maki 6, ya yinda Akwa take da 4, Lobi a matakin ƙarshe bata da maki ko daya.