Hukumar kiyaye aukuwar hadura reshen jihar Bauchi, ta tabbatar da rasuwar mutane 16, a wani hadarin mota da aka yi a kauyen Bambal dake kan hanyar Kano zuwa Jama’are.
Kwamandan Hukumar a jihar Bauchi Yusuf Abdullahi, shine ya bayyana hakan a wata tattauna da yayi da kamfanin dillacin labarai na kasa NAN.
Ya ce hadarin ya faru ne a ranar lahadin da ta gabata da misalin karfe karfe 7 na dare, tsakanin wata babbar mota da kuma wata mota kirar Toyota Hummer bus, inda karamar motar ta kama da wuta bayan tayi karo da babbar.
Ya kara da cewa, bayan faruwar lamarin da minti 7 jami’an hukumar sun isa wajen, inda suka tarar gaba daya mutane 16 da abun ya rutsa dasu sun rasu, maza 10 mata 6.
Kwamandan Hukumar a jihar Bauchi ya alakanta lamarin da tukin ganganci, yana mai tabbatar da cewa Tuni aka kai gawarwarkin mutanen zuwa babban Asibitin Kiyawa dake kan titin Kano zuwa Jama’are.













































