Hukumar NDLEA ta tarwatsa wani bikin daurin aure a Katsina inda aka gudanar da gasar shan miyagun kwayoyi a wata unguwa Shola Quarters.
An kama matasa 25 da suka halarci gasar.
Mai magana da yawun hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi shi ne ya bayyana hakan ranar lahadi a Abuja.
Femi, yace mahalarta taron suna bi da bi ne wajen shan miyagun kwayoyi da aka jika a cikin bokitin roba a lokacin da jami’an suka kai sumame.
Ya kara da cewa an kama mutane uku da ake zargi da suka hadar da Monday John mai shekaru 50.
Karanta wannan:Mutum 16 sun mutu yayin da 27 suka ji raunuka a hadarin mota
Sai Maryam Adang mai shekaru 48, da Mohammed Musa mai shekaru 36, a sassa daban-daban na jihar Kaduna a tsakanin ranar 7 zuwa 9 ga watan Disamba.
Ya kara da cewa an kama Adamu Nuhu mai shekaru 20 a ranar Litinin, 3 ga watan Disamba a kan hanyar Okene zuwa Lokoja zuwa Abuja yayin da yake dawowa daga Onitsha ya nufi Kaduna.