Hukumar kiyaye aukuwar haddura ta kasa FRSC reshen jihar Kaduna, ta tabbatar da mutuwar mutane 16.
Haka kuma 27 suka samu raunuka a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Kwamandan sashin, Kabir Nadabo, ya ce hatsarin ya auku ne a ranar Lahadi, da misalin karfe 5 da mintuna 20 na asubah.
Karanta wannan:Sojojin sun halaka ‘yan ta’adda ta hanyar yi musu luguden wuta ta sama a jihar Neja

Ya kara da cewa tun da farko wata mota kirar DAF ce mai lamba KUJ 430XC, dauke da kaya, ta fada cikin rami.
Nadabo ya ce da samun labarin afkuwar hatsarin, jami’ansu sun ziyarci wurin domin aikin ceto.













































