Sojojin sun halaka ‘yan ta’adda ta hanyar yi musu luguden wuta ta sama a jihar Neja

NAF neutralised terrorist kingpin Yellow Jambros and others in air strike
NAF neutralised terrorist kingpin Yellow Jambros and others in air strike

Rundunar Sojin saman Najeriya ta samu nasarar kama ‘yan ta’adda tare da hallaka wasu da dama ta hanyar yi musu luguden wuta ta sama a karamar hukumar Shiroro da ke Jihar Niger.

Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da Yan ta’addar ke shirin tsallakawa zuwa karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna ta ruwa.

Ta cikin wata sanarwa da darakran yada labaran rundunar Edward Gabkwet ya fitar da sanyin safiyar ranar Lahadi, yace lamarin ya faru ne a ranar Larabar da ta gabata bayan da jami’an rundunar na Operation Whirl Punch suka kaddamar da harin akan ‘yan ta’addan.

Karanta wannan:Gwamna Radda zai bincike wadanda suka ci gajiyar shirin Anchor Borrowers  

A cewarsa dakarun sojin sun samu nasarar hallaka kasurgumin dan ta’addan nan da ake kira da suna Yellow Jambros tare da gun-gun wasu ‘yan ta’adda akan babura da suka fito daga jihar Zamfara.

Rundunar Sojin saman dai tace ‘yan bindigar wadanda suke haye akan babura suna shirin ficewa daga jihar ta Niger zuwa karamar hukumar Chikun dake Jihar Kaduna ta cikin ruwa, tuni sun bakwanci barzahu bayan sun kaddamar musu da luguden wuta ta sama.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here