Gwamna Yusuf ya yabawa hukumar PCACC kan yaki da cin hanci da rashawa

FB IMG 1699444381726 750x430
FB IMG 1699444381726 750x430

Gwamnatin jihar Kano ta ce, bazata saurarawa duk wani jami’in gwamnati da aka samu da karbar cin hanci da rashawa ko bayarwa ba.

Mataimakin gwamnan jihar Kano Kwamred Aminu Abdulsalam ne ya bayyana hakan a madadin gwamna Abba Kabir Yusuf, a wani bangare na bikin ranar yaki da cin hanci da rashawa da aka gudanar.

Gwamnan ya yaba da kokarin hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano a yaki da cin hanci da rashawa ba dare ba rana.

Gwamnan ya kuma tabbatar da cewa ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen ganin sun kawar da cin hanci da rashawa a jihar.

Karanta Wannan:Gwamna Yusuf ya nada manyan sakatarori 21, tare da sake sauyawa wasu 8 wuraren aiki

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa taken bikin na bana shi ne “Hadin kan al’ummar duniya domin yakar cin hanci da rashawa”

Barrister Muhyi Magaji Rimin Gado

A nasa jawabin, Shugaban hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa Muhuyi Magaji Rimingado ya ce makasudin taron shi ne tunawa da ranar cin hanci da rashawa ta duniya da kuma yin amfani da wannan damar wajen wayar da kan jama’a kan illolin cin hanci da rashawa.

A nasa bangaren, kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Muhammed Usaini Gumel, ya jaddada muhimmancin yin garambawul da sake farfado da muhimman sassa domin yaki da cin hanci da rashawa yadda ya kamata a matakin jiha da kasa baki daya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here