Bata gari sun lalata layin wutar Lokoja–Gwagwalada

power supply 750x430 (1)

Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya sanar da sake kai farmaki ga layin 330kV na Lokoja–Gwagwalada da wasu ‘yan ta’adda suka lalata.

Wannan na zuwa ne yayin da ‘yan Najeriya ke jiran dawowar wutar lantarki bayan harin baya-bayan nan a kan layin wutar 330kV na Shiroro-Kaduna.

A cikin wata sanarwa da Babbar Manajan Hulɗa da Jama’a na TCN, Ndidi Mbah, ta fitar a ranar Lahadi, kamfanin ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Asabar, 9 ga Nuwamba, 2024.

‘Yan ta’addan sun lalata ginshiƙai na wutar lantarki na T306, T307, da T308, wanda ya jawo katsewar wutar lantarki a kan wannan layi.

Kokarin injiniyoyin TCN na mayar da layin aiki a safiyar Asabar ya ci tura yayin da aka samu matsala kan layin.

Binciken da tawagar TCN ta gudanar ya tabbatar da wannan lalacewa, ciki har da satar kebul biyu na ƙarfen aluminium.

Duk da yake layin wutar na igiya biyu ne, kuma har yanzu yana aiki ta wata hanyar daban, kamfanin yana ci gaba da neman ma’aikatan da za su maye gurbin sassan da aka sace.

Wannan lamari yana daga cikin munanan hare-hare da ke yawaita kan kayayyakin rarraba wutar lantarki a Najeriya, musamman a yankin Gwagwalada.

A baya an samu irin wannan harin a kan layin Gwagwalada–Kukuwaba–Apo a ranar 10 ga Disamba, 2023, da kuma layin Gwagwalada–Katampe a ranar 26 ga Fabrairu, 2024.

Irin wadannan hare-hare na ci gaba da haifar da matsalar rashin kwanciyar hankali da bunkasar layin rarraba wutar lantarki a kasar.

TCN ta sake yin kira ga al’ummomin da ke kusa da wuraren rarraba wutar tare da hukumomin tsaro da su hada kai don magance wannan matsala ta lalata kayayyakin wutar.

Kamfanin ya jaddada cewa wadannan ayyukan suna raunana kokarin inganta tsarin rarraba wutar lantarki a Najeriya, kuma babban rashin adalci ne ga al’umma baki daya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here