Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce jami’anta sun kama wasu mutane biyu da ake zargin masu lalata titin jirgin kasa ne tare da kwato karfen titn guda 40 a ranar Asabar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, ASP Mansir Hassan, ya tabbatar da faruwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Lahadi a Kaduna.
Ya bayyana sunayen wadanda ake zargin Joel Musa da John Yakubu dukkansu daga kauyen Pakau da ke karamar hukumar Kagarko.
Ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike, yana mai cewa, za a gurfanar da su gaban kotu domin gurfanar da su gaban kuliya.