
Rahoton SolaceBase kan rahoton aikin kasafin kudin Jihar Neja ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta kashe naira biliyan 1.2 a kan bukukuwa da wasu ranaku na musamman cikin watanni tara na farkon shekarar 2024.
Wannan kashe kudi yana wakiltar kimanin kaso 4% na kudaden shiga na cikin gida da jihar ta samu wanda ya kai naira biliyan 29.2 daga Janairu zuwa Satumba.
Wannan kashe kudin ya haifar da damuwa, musamman ma ganin yadda jihar ke fuskantar matsalolin tsaro da kuma na ci gaban al’umma.
A kwanakin baya, jihar Neja ta fuskanci hare-haren ‘yan bindiga, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane goma tare da lalata gidaje.
Bugu da ƙari, ambaliyar ruwa ta rusa fiye da ƙauyuka 300 a jihar, inda rahotanni suka bayyana cewa mutane goma sha ɗaya sun rasa rayukansu yayin da aka lalata makarantu 245.
Duk da wadannan kalubale, kasafin kudin ya nuna cewa ba a ware ko naira daya ba ga ayyukan manyan abubuwan gina na Ma’aikatar Raya Karkara da Hukumar Ruwa da Tsabtace Muhalli.
Wannan rashin tallafin ya zo a daidai lokacin da annobar cutar kwalara ta yi ajalin mutane goma sha shida tare da shafar wasu mutane 165.
Mutane da dama sun koma amfani da ruwan da ke tsaye ko kuma wanda suke rabawa da dabbobi, saboda rashin ruwan sha mai tsafta.
A gefe guda kuma, Ma’aikatar Ilimin Firamare da Sakandare ta samu naira miliyan 196 kacal a bangaren ayyukan manyan abubuwa, yayin da bangaren kiwon lafiya na asali ya rasa tallafin kudi na ayyukan inganta gine-gine.
Rahotanni sun nuna cewa kashi 71% na gidaje a jihar na fama da rashin wuraren tsabtace muhalli, sannan rabin al’ummar jihar na fama da rashin samun ruwan sha mai tsafta, abin da ya nuna bukatar kudaden zuba jari a ayyukan da ake buƙata.
Duk da ikirarin karancin albarkatu, yadda Jihar Neja ta sanya fifiko kan abubuwan da take kashe kudi ya haifar da damuwa.
A yanzu haka, jihar na da mutane miliyan 1.6 dake fama da talauci yayin da matsalar rashin aikin yi ta kai kashi 38.8%.