Cibiyar inganta fasahar sadarwa da ci gaban al’umma (CITAD) ta yi Allah-wadai da kame ɗalibin digiri na biyu na sashen tattalin arziƙin noma a jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida da ke Lapai, Abubakar Isah Mokwa, bisa zargin sukar Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, a dandalin Facebook.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, an kama ɗalibin ne a masaukinsa da ke wajen harabar jami’a a Lapai, inda daga nan aka tura shi hedkwatar rundunar ‘yan sanda ta Jihar Neja da ke Minna, bisa umarnin gwamnan.
CITAD ta bayyana cewa jami’an ‘yan sanda sun ce an kama shi ne bisa zargin “cin zarafi da tsoratarwa ta hanyar amfani da internet”, sai dai cibiyar ta ce wannan yunƙuri ne na hana ‘yancin faɗar albarkacin baki da murkushe masu suka a jihar.
A cikin sanarwar da daraktan gudanarwa na CITAD, Y.Z. Ya’u, ya fitar, ya bayyana cewa kama ɗalibi saboda bayyana ra’ayinsa ya sabawa sashe na 39 na kundin tsarin mulkin ƙasar Najeriya na shekarar 1999 (da aka gyara), wanda ke tabbatar da ‘yancin faɗin albarkacin baki da riƙe ra’ayi ba tare da tsangwama ba.
CITAD ta kuma tunatar da cewa wannan ba shi ne karo na farko ba da gwamnatin Umaru Bago ke murkushe kafafen watsa labarai da ‘yan jarida a jihar.
A watan Agusta 2025, gwamnatin ta dakatar da tashar Badegi 90.1 FM saboda sukar gwamnati, yayin da wasu ‘yan jarida daga Peoples Daily da Muryar Amurka suka fuskanci barazana da duka yayin aikin su.
CITAD ta bukaci a saki Abubakar Isah Mokwa ba tare da wani sharadi ba, tare da kira ga gwamnatin tarayya da shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu da su tabbatar cewa ‘yan sanda ba sa amfani da iko wajen kama jama’a saboda bayyana ra’ayinsu.
Ta kuma shawarci Gwamna Bago da ya mutunta ‘yancin faɗar albarkacin baki, tare da mai da hankali wajen inganta ci gaban jihar maimakon tsoratar da matasa da ‘yan jarida.













































