Farfesa M. K. Othman ya zama sabon shugaban jami’ar FUDMA

Prof. M.K Othman new 720x430

Majalisar gudanarwar jami’ar tarayya ta Dutsin-Ma (FUDMA) ta amince da naɗin Farfesa Mohammed Khalid Othman a matsayin sabon shugaban jami’ar.

Shugaban majalisar gudanarwa kuma mai ba da shawara ga jami’ar, Ambasada Ali Abubakar Jatau, ne ya sanar da haka bayan kammala taron musamman na 36 da aka gudanar a Dutse, Jihar Jigawa.

Sanarwar da daraktan yada labarai na jami’ar, Nasiru M. Abdul, ya fitar a ranar Juma’a ta bayyana cewa naɗin ya biyo bayan rahoton kwamitin haɗin gwiwa na majalisar gudanarwa da ta malamai kan zaɓen sabon shugaban jami’a.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa Farfesa Othman ya fito ne bayan gudanar da cikakken tsarin zaɓe da ya haɗa da masu neman mukamin 17 daga cikin mutum 28 da suka nuna sha’awa.

Farfesan, wanda aka haifa a ranar 22 ga Yuli, 1962, a ƙaramar hukumar Bindawa ta Jihar Katsina, injiniya ne a fannin noma da ya yi karatunsa na farko, na biyu da na uku a jami’ar Ahmadu Bello Zaria.

Ya yi aiki daga matsayin mataimakin malami zuwa farfesa, tare da riƙe mukamai daban-daban a matsayin malami, mai bincike da kuma mai gudanarwa.

Farfesa Othman ya kasance tsohon darakta janar na cibiyar binciken yada sabbin hanyoyin aikin gona (NAERLS) ta jami’ar Ahmadu Bello Zaria, kuma a yanzu mamba ne na majalisar gudanarwar jami’ar FUDMA daga bangaren majalisar malamai.

Sabon shugaban jami’ar yana da mata da ‘ya’ya tara.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here