NNPP ta koka kan shirin Jam’iyyar APC na tafka magudi a zaben kujerar fagge da za a sake

NNPP APC 750x430 1
NNPP APC 750x430 1

Jam’iyyar NNPP ta koka kan wani shiri da ake zargin jam’iyyar APC mai mulki da yi na yin magudi a zaben da aka kammala na mazabar Fagge, inda ta ce ba za su amince da duk wani yunkuri na kawo cikas a zaben ba.

Jaridar Solacebase ta bada rahoton cewa INEC ta bayyana zaben dan majalisar wakilai na Fagge a matsayin wanda bai kammala ba sakamakon kada kuri’a da kuma hargitsa zaben da aka yi a mazabu goma sha biyar a fadin karamar hukumar.

Da yake jawabi ga manema labarai a yammacin ranar Asabar, Shugaban Jam’iyyar NNPP, a Jihar Kano, Hon. Umar Haruna Doguwa ya ce sun samu rahoton cewa gwamnatin jihar Kano na shirin kawo cikas da magudin zabe, duk da cewa ta mamaye matsayi na uku a zaben ‘yan majalisar dokokin kasar da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

“Kafin soke sakamakon zaben, dan takarar jam’iyyar NNPP yana kan gaba da kuri’u dubu biyar da dari shida da hamsin da takwas, sai kuma LP sai APC, amma jam’iyya mai mulki, APC na kokarin amfani da wasu ma’aikatan INEC da jami’an tsaro su tayar da hankula domin a bayyana dan takararsu a matsayin wanda ya lashe zaben,” inji Shugaban NNPC.

‘’Duk kun san cewa an gudanar da zaben a ranar 25 ga Fabrairu, 2023 don zaben dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Fagge ta Jihar Kano inda dan takarar jam’iyyar NNPP Barr. Muhammad Bello Shehu Fagge, ya samu kuri’u 18, 415 wanda ya kasance mafi girma a cikin manyan jam’iyyun; Labour Party (LP)-12,729, APC –8,394 da PDP 6,546 kamar yadda jami’in tattara bayanan, Farfesa Shehu Usman Yahya na Jami’ar Bayero Kano ya sanar.’’

‘’Sakamakon rumfuna goma sha biyar (15) da INEC ta soke sakamakon kada kuri’a da kuma kawo cikas da aka samu. Wadannan sun hada da: Army Day Primary School II-004, Gobirawa Primary School II-018, Jaba II-020, Kofar Dan Rimi I-023, Kofar Maiungwa-025, Kurna Gabas I-026, Kurna Gabas V–30, Mami Market IV. -040, Kasuwar Mami II-042 Sabontiti D/Rimi-047, Sakwaya-048, Hajaratu Islamiyya-080, Kwanar Dan Rimi I-011, Kwanar Dan Rimi III-013, Asibitin Aminu-031.”

Jam’iyyar ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, jami’an tsaro, masu sa ido kan zabe, da sauran jama’a da su sanya ido ga INEC a zaben cike gurbi na mazabar Fagge da ke tafe.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here