Rikicin APC: INEC ba ta amince da Sani Bello ba, ta ki amincewa da taron NEC da aka shirya gudanarwa

Sani Bello and Mai Mala Buni 1
Sani Bello and Mai Mala Buni 1

 

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta yi watsi da jadawalin taron majalisar zartaswa na APC da za a yi a mako mai zuwa karkashin jagorancin Gwamna Abubakar Sani Bello, a matsayin shugabanKwamitin Tsare-tsare na Musamman na jam’iyyar.

Solacebase ta ruwaito cewa Hukumar ta yi watsi da wasikar jam’iyyar mai kwanan wata 8 ga Maris, 2022 mai taken ”Gayyatar taron gaggawa na kwamitin zartarwa na kasa”.

Idan dai za a iya tunawa Gwamna Sani Bello ya karbi ragamar shugabancin jam’iyyar ne a ranar Litinin 7 ga watan Maris a wani yanayi mai cike da cece-kuce da ya ce an kori Mai Mala Buni a matsayin shugaban jam’iyyar da izinin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Duk da cewa wata wasika da Mai Mala Buni ya rubuta kafin ya fita kasar, ya nuna cewa ya mika wa Sani Bello a matsayin mataimakin shugaban kasa kafin tafiyar tasa.

A cikin wata wasika da ta aike wa shugaban jam’iyyar shugabancin APC mai kwanan wata 9 ga Maris, 2022 mai dauke da sa hannun Sakatariyar Hukumar, Rose Onaran-Anthony, INEC ta ja hankalin jam’iyyar dangane da sanarwar taron ta samu sa hannun shugaba da sakataren CECPC sabanin tanadin sashe na 1.1.3 na dokokin hukumar da ka’idojin gudanar da harkokin jam’iyyun siyasa (2018).

Wasikar ta kara da cewa, ”Bugu da kari kuma, jam’iyyar APC ya kamata ta tuna da tanadin sashe na 82(1) na dokar zabe ta 2022 wanda ke bukatar ”a kalla kwanaki 21” na duk wani babban taro don manufar ”haɗin kai” da zaɓen mambobin kwamitin zartarwa.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here