Yajin aiki: ASUU ta soki COPSUN kan kalaman ta a yunkurin warware yajin aiki

ASUU ASUU NEW
ASUU ASUU NEW

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta shawarci kwamitin da ke kula da jami’o’in jihohi (COPSUN) da su daina wasa kan batun tattaunawa dan shawo kan yajin aiki.

Wannan na kunshe ne a cikin wani kundi da Farfesa Ade Adejumo ya gabatar mai taken: “Yadda za a warware takaddama mai zafi”

Adejumo ya ce babu wata barazana da za ta sa kungiyar ta daina fafutukar ganin an samar da ingantaccen ilimi da walwalar mambobinta.

Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, ASUU na mayar da martani ne ga sanarwar da aka fitar a karshen taron COPSUN inda suka ce ya kamata gwamnati ta aiwatar da “Ba A Aiki Ba Biyan albashi”.

Adejumo ya ce akwai bukatar COPSUN ta fahimci cewa doka ta amince da tsarin hada-hadar gudanar da aiki tareda biyan albashi aduk halin da ake ciki.

Adejumo ya ce masu goyon bayan shugabannin jami’o’in jihohi “a koda yaushe suna zagin su gudu zuwa Abuja domin karbar kudi daga TETFUND da ASUU ta kawo.

ASUU ta ce ya kamata kwamitin ya yi koyi da takwarorinsu na jami’o’in Tarayya da ke jan hankalin gwamnati wajen yin abubuwan da ake bukata ga jami’o’in gwamnati.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here