Hukumar kulada sufurin jirage ta kasa ta dakatar da lasisin AZMAN saboda rashin biyan wasu kudade

AZMAN New 1
AZMAN New 1

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya NCAA ta dakatar da lasisin zirga-zirgar jiragen sama na kamfanin Azman Air saboda gazawa ta biya kudin siyar da tikitin tikitin Naira miliyan dubu 1200 daga fasinjoji.

Babban Daraktan hukumar Kyaftin Musa Nuhu ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ikko

Nuhu ya yi bayanin cewa an dakatar da kamfanin ne saboda rashin bayar da takardur tsaro don sabunta tsarin sa na ATL dinsa wanda ya kare a watan Afrilun 2021.

Nuhu ya ce bashin Naira biliyan 1 da dubu 200 shi ne kudaden shiga da aka samu daga cikin kashi biyar na kudin siyar da tikiti da kuma na sayar da kaya da kamfanin ke karba daga hannun matafiya.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bada rahoton cewa ana raba kudaden ne tsakanin hukumomin jiragen sama guda biyar; NCAA da Hukumar Kula da Sararin Samaniya ta Najeriya.

Sauran sun hada da Hukumar Binciken Hatsari, Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMET) da Kwalejin Fasahar Jiragen Sama ta Najeriya ta Zariya.

Hukumar NCAA tana samun kashi 58 cikin 100 daga jimillar kashi 5 yayin da sauran hukumomi hudu ke raba sauran kashi 42 cikin 100.

Nuhu ya koka da cewa hukumar ta yi kokarin kwato basussukan da kamfanin ke bin kamfanin tsawon shekaru. Shi dai Kamfanin Azman ya fara ayyukan sa a shekarar 2014.

Babban Daraktan ya ce: “Ba mu dakatar da takardar shaidar jigilar Kamfanin Azman ba, amma mun dakatar da tsarin su na ATL dinsu, wanda a baya ya kare.

Nuhu ya kuma yi barazanar cewa ba za a sabunta ATL na duk wani kamfanin jirgin da ke bin hukumar bashin kashi biyar ba.

Yayi kira ga sauran abokan hulda dake jigilar sifiri dasu biya basussukan da ake bin su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here