Kamfanin Azman ya bayyana dawowar sa hada-hadar aikin jigila

AZMAN New 1
AZMAN New 1

Kamfanin jiragen sama na Azman ya sanar da dawowa da aikin zirga-zirgar jiragensa bayan dakatarwar da hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya ta yi.

Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya ta dakatar da lasisin zirga-zirgar Jiragen Sama na kamfanin Azman saboda gazawa wajan biya Naira biliyan 2 da doriya na tikitin fasinjoji.

Babban Daraktan Hukumar Kyaftin Musa Nuhu ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ikko

Sai dai wata majiya da kamfanin AZMAN ya fitar, ya shaidawa Solacebase a daren Alhamis cewa kamfanin ya tattauna da NCAA a yau wanda hakan ya kai ga dage dakatarwar da aka yi wa kamfanin.

Ya ce lamarin dage lasisin ya kai ga fitar da jadawalin tashi daga gobe da kamfanin jirgin ya yi.

Kamfanin Jiragen Sama na Azman ashafin na Twitter ya ce, “An dawo da aikin kuma a yanzu haka dukkan jirage za su yi cigaba da aikin jigila kamar yadda aka tsara daga ranar Juma’a 16 ga Satumba.”

”Saboda haka muna fatan duk Fasinja zasu lura da kyau”.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here