Shugaban majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya buƙaci shugaban ƙasa Bola Tinubu ya sake duba umarnin da ya bayar na janye jami’an ‘yan sanda daga ba da tsaro ga manyan mutane masu muƙami a ƙasar.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa shugaban ƙasa ya bayar da umarnin janye jami’an ‘yan sanda da ke kare manyan mutane, domin a tura su su taimaka wajen shawo kan matsalolin tsaro da ke addabar ƙasa.
Bisa wannan umarni, duk wanda ke buƙatar kariya zai nemi jami’an tsaro masu makamai daga hukumar tsaron fararen hula ta Najeriya maimakon ‘yan sanda.
Akpabio ya bayyana buƙatar sake duba wannan mataki ne a yayin zaman haɗin gwiwa na majalisar dokoki ta ƙasa, jim kaɗan bayan shugaban ƙasa ya gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2026.
Karanta: Shugaba Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2026 na sama da Naira Tiriliyan 58
Ya nuna damuwa cewa matakin ya jefa ‘yan majalisar tarayya cikin barazanar tsaro.
A cewarsa, janye jami’an tsaro daga ‘yan majalisa ya sa wasu daga cikinsu ke fuskantar matsaloli na tsaro, har ta kai suna nuna fargabar komawa gidajensu sakamakon yiwuwar fuskantar haɗari.
Shugaban majalisar dattawan ya roƙi shugaban ƙasa da ya sake duba wannan shawara domin tabbatar da lafiyar ‘yan majalisar dokoki da sauran muhimman jami’an gwamnati, tare da la’akari da halin tsaro da ake ciki a ƙasar.
Akpabio ya kuma yaba wa shugaban ƙasa bisa sauye-sauyen tattalin arziƙi da gwamnatinsa ta aiwatar tun bayan hawansa mulki, yana mai cewa sauye-sauyen sun fara haifar da sakamako mai kyau.
Ya tabbatar da cewa majalisar dokoki ta ƙasa na tare da shugaban ƙasa wajen aiwatar da manufofin da za su kawo zaman lafiya, tsaro da ci gaban ƙasa.










































