Cibiyar bunƙasa fasahar sadarwa da ci gaban al’umma CITAD ta bayyana damuwa kan zargin da ke nuna cewa sigogin dokokin gyaran haraji da aka wallafa a kundin dokoki na hukuma sun bambanta sosai da waɗanda majalisar dokoki ta ƙasa ta tattauna, ta amince da su, kuma ta zartar.
Daraktan zartarwa na CITAD YZ Ya’u ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu, biyo bayan batun da aka taso da shi a zaman majalisar wakilai, inda wani ɗan majalisa Abdulsamad Dasuki ya yi zargin cewa wasu da ba a bayyana su ba sun karya ikon majalisa ta hanyar sauya muhimman tanade-tanaden dokokin harajin bayan an riga an amince da su a majalisun biyu.
CITAD ta jaddada cewa waɗannan zarge-zargen na haifar da manyan matsaloli na kundin tsarin mulki, doka da dimokuraɗiyya, waɗanda ke buƙatar kulawa cikin gaggawa.
Ta bayyana cewa a ƙarƙashin kundin tsarin mulkin Najeriya, ikon yin doka na hannun majalisar dokoki ta ƙasa kaɗai, kuma duk wani sauyi da aka yi bayan zartar da doka ba tare da bin tsarin majalisa ba kutse ne ba bisa ƙa’ida ba cikin ikon majalisa, tare da karya ka’idar raba iko.
Cibiyar ta ƙara da cewa binciken farko da aka yi kan dokokin harajin da aka wallafa ya nuna cewa bambance-bambancen da ake zargi ba na gyaran rubutu kawai ba ne, illa dai sauye-sauye ne masu muhimmanci da ka iya sauya manufar doka, matakan kariya da sakamakon shari’a kamar yadda majalisar dokoki ta ƙasa ta zartar.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa CITAD ta lura da cewa daga cikin wuraren da ake zargi akwai tanade-tanade kan lissafin haraji, hanyoyin ɗaukaka ƙara da ikon tilastawa, inda wasu ke faɗaɗa ikon hukumomin haraji tare da raunana sa ido na kotuna da kariyar masu biyan haraji.
Ta ce idan aka tabbatar da hakan, zai iya lalata bin doka da oda tare da rage amincewar jama’a ga shirin gyaran haraji.
Duk da maraba da matakin majalisar wakilai na kafa kwamitin wucin gadi domin binciken lamarin, CITAD ta ce girman zarge-zargen na buƙatar tsarin bincike a bayyane, mai gaskiya kuma mai iyaka da lokaci, wanda zai iya dawo da amincewa ga tsarin majalisa.
Ta buƙaci a wallafa cikakkun bayanan zaman majalisa da rubuce-rubucen da suka shafi dokokin gyaran haraji, tare da sigogin dokokin da aka wallafa, domin bai wa ’yan Najeriya damar kwatanta abin da aka tattauna da abin da aka wallafa a matsayin doka.
CITAD ta kuma nemi a dakatar da aiwatarwa da tilasta dokokin gyaran harajin gaba ɗaya, ciki har da ranar fara aiki da aka tsara, har sai an kammala binciken.
Ta gargaɗi cewa ci gaba da aiwatarwa a cikin yanayin zargin rashin bin doka na iya haifar da shari’o’i, rikice-rikicen doka da ƙarin asarar amincewar jama’a.












































