Jam’iyyar NNPP ta bayyana cewa tana ci gaba da kasancewa ƙarfi mai ɗorewa da ba za a tsoratar ko a yi mata razana ba a fagen dimokuraɗiyya da siyasar Najeriya.
Shugaban jam’iyyar na ƙasa Dakta Ahmed Ajuji ya bayyana hakan yayin jawabinsa a taron kwamitin zartarwa na ƙasa NEC na jam’iyyar da aka gudanar a Abuja.
Ya nuna cewa duk wani yunkuri daga waje ko cikin gida na rarraba jam’iyyar da shugabanninta domin raunana ta bai yi nasara ba.
Ya jaddada cewa jam’iyyar ba ta karkata ga kowa ko bin umarnin wasu kamar yadda wasu jam’iyyu ke yi ba, yana mai bayyana NNPP a matsayin jam’iyya mai haɗin kai da mayar da hankali kan manufofinta.
A cewarsa, jam’iyyar tare da mambobinta masu ƙaruwa a faɗin ƙasar za ta ci gaba da zama ginshiƙin haɗin kai da zai kai ta ga nasara a zaɓen 2027.
Dakta Ajuji ya kuma bayyana cewa taron NEC ɗin shi ne na ƙarshe ga mambobin kwamitin aiki na ƙasa NWC na yanzu a ƙarƙashin jagorancinsa.
Ya nuna gamsuwa da cewa shugabancinsa bai gaza wa jam’iyyar ba, tare da fatan cewa da dama daga cikinsu za su ci gaba da yi wa jam’iyyar da ƙasa hidima.
Ya yaba da jagoranci da shawarwarin shugaban jam’iyyar na ƙasa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da kuma goyon bayan gwamnan jihar Kano da sauran shugabanni da mambobin jam’iyyar.
Ya kuma buƙaci shugabanni da mambobi su yi watsi da dabarun wasu mambobi da aka dakatar da ke ikirarin ficewa domin raunana jam’iyyar.
A nasa jawabin, Rabiu Musa Kwankwaso ya taya shugabannin jam’iyyar masu barin gado murna, musamman kan nasarar gudanar da tarukan jam’iyya a matakin unguwanni, ƙananan hukumomi da jihohi.
Ya bayyana NNPP a matsayin ɗaya daga cikin manyan jam’iyyu a Najeriya, yana mai cewa ba yawa ne ke kawo ƙarfi ba, illa haɗin kai da tsari.
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ta bakin mataimakinsa Aminu Gwarzo, ya ce duk da ƙalubalen da jam’iyyun adawa ke fuskanta, NNPP na ƙara ƙarfi tare da gina kan nasarorin da ta samu.
Ya nuna cewa irin yadda jam’iyyar ke tafiyar da al’amuranta ya sa ba wata jam’iyya da za ta iya yin gogayya da ita.
Sakataren jam’iyyar na ƙasa Dipo Johnson ya yaba wa bangaren shari’a da hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC kan kiyaye doka da oda a batutuwan da suka shafi jam’iyyar.
Ya bayyana cewa NNPP ta samu nasarar gudanar da zaɓukan shugabanni a matakin unguwa da jiha a dukkan jihohi 36 da babban birnin tarayya.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa taron ya amince da sakamakon zaɓukan shugabanni na unguwa, ƙananan hukumomi da jihohi, da na yankuna shida, tare da tabbatar da gudanar da babban taron jam’iyyar a ranar 20 ga Disamba, da kuma amincewa da dakatar da sashe na 37(1) na kundin tsarin jam’iyyar NNPP na shekarar 2024 kamar yadda aka yi masa gyara.













































