Kotu ta hana CBN da wasu hukumomin tarayya rike kudin kananan hukumomin jihar Kano

court
court

Kotun koli ta jihar Kano ta bayar da umarnin hana wasu hukumomin tarayya tsaida ko rike kudaden da ake tura wa kananan hukumomi 44 na jihar Kano a kowane wata.

Wannan hukunci ya biyo bayan ƙarar da Ƙungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumomi (NULGE) da wasu mazauna jihar suka shigar inda suka nuna damuwa kan yiyuwar tsaida kudaden da ake bai wa kananan hukumomin don gudanar da ayyukansu.

Mai shari’a Ibrahim Musa Muhammad ya ba wa masu shigar da ƙarar damar isar da takardun shari’a ga Ofishin Akanta Janar na Tarayya, CBN, RMAFC, da wasu bankuna.

Kotu ta nada kamfanin Red Star Express Plc don tabbatar da isar takardun ga waɗannan hukumomin da ke wajen jihar Kano.

Wannan umarnin na wucin gadi ya hana hukumomin tarayya yin wani abu da zai iya hana ko tsaida kudaden kananan hukumomin har zuwa ranar 21 ga Nuwamba, 2024, lokacin da za a ci gaba da sauraron ƙarar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here