Kano: kotu ta yanke wa wani mutum hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa zargin kashe makocinsa

Hanging rope 1

Kotu a jihar Kano ta yanke wa wani matashi mai suna Najibullah Alkasim hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin kashe makocinsa Isyaku Ya’u da wani ƙaramin sanda da ya soka masa.

Alkasim, wanda mazauninsa ke unguwar Dakata a cikin ƙaramar hukumar Nasarawa, an same shi da laifin kisan kai da gangan bayan shari’a ta tabbatar da hujjojin da aka gabatar a kansa.

Alƙaliyar da ta yi hukuncin, Mai shari’a Farida Danbappa, ta tabbatar da cewa hujjojin da masu gabatar da ƙara suka gabatar sun wadatar wajen tabbatar da laifin ba tare da wani shakku ba.

Wannan ya haɗa da bayanan likita, hoto, makamin da ake zargin an yi amfani da shi, da kuma bayanin amincewa da laifin da aka ce an samu daga Alkasim.

Hukumar gurfanarwa ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a cikin unguwar Dawakin Dakata lokacin wani taron murnar nasarar kotun zaɓe, inda rashin jituwar da ta taso tsakanin Alkasim da mamacin ya rikide zuwa tashin hankali.

A lokacin rikicin ne Alkasim ya soki mamacin a kirji da mugun abu mai kaifi wanda ya yi sanadin mutuwarsa.

Masu gabatar da ƙara sun ce laifin ya sabawa sashe na 221(a) na kundin hukunta laifuka na ƙasa, kuma sun gabatar da shaidu huɗu domin tabbatar da tuhumar.

Sai dai wanda ake tuhuma ya musanta aikata laifin gabaki ɗaya duk da shaidun da aka gabarar masa da su.

Lauyan karita ga wanda ake tuhuma, Tasiu Daneji, ya gabatar da Alkasim tare da wasu shaidu biyu domin kare shi daga tuhumar da ake masa.

Sai dai bayan nazarin hujjoji, kotu ta tabbatar da laifin tare da hukunta shi da hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa tanadin doka.

Hukumar gurfanarwa ta bayyana cewa wannan hukunci na daga cikin ƙoƙarin tabbatar da doka da oda tare da kare rayukan al’umma daga rikice-rikicen da ke jawo salwantar rayuka a cikin unguwannin birnin Kano.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here