Sabon rikicin kan jagoranci ya kunno kai a cikin jam’iyyar NDC a Jihar Kano, inda manyan jami’an jam’iyyar suka zargi tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da kokarin mamaye tsarin jam’iyyar da watsar da sauran masu ruwa da tsaki.
Zargin na kunshe ne a cikin wani sakon korafi da aka ce mataimakin shugaban jam’iyyar na Arewa maso Yamma, Mohammed Serina, da shugaban jam’iyyar na Jihar Kano, Hussaini Mariga suka mika wa shugaban jam’iyyar na kasa Seriake Dickson.
Shugabannin jam’iyyar sun ce duk da sun marabci Kwankwaso da magoya bayansa a NDC tare da ba su tasiri mai yawa, ana zargin yana kokarin daukar cikakken iko da tsarin jam’iyyar a Kano.
Da yake bayani kan lamarin, Serina ya ce rashin jituwar ya bayyana ne a lokacin zaben fidda gwani na jihar, inda suka damu kan yadda ake raba iko a cikin jam’iyyar.
A cewarsa, zaman sulhu da shugabancin jam’iyyar na kasa ya yi ya yanke cewa Kwankwaso da mambobin kungiyar Kwankwasiyya za su rike kashi 60 na tsarin jam’iyyar a Kano, yayin da sauran kashi 40 za su kasance na sauran masu ruwa da tsaki.
Sai dai ya zargi cewa ba a mutunta yarjejeniyar ba a lokacin tsarin zaben ‘yan takara, inda ya ce samun ffom din zabe ne ya fara haifar da matsala.
Serina ya zargi cewa an tara fom din zabe ne a hannun bangaren Kwankwasiyya, lamarin da ya bar sauaran ‘yan jam’iyya da masu neman takara da yawa wadanda ba na bangaren ba samun damar shiga zaben fidda gwani yadda ya kamata.
Ya kara da cewa an yi watsi da korafe-korafen da ake yi na a samu tsarin da zai hada kowa, duk da bukatar a ware wani kaso na fom din zabe ga wadanda ba na Kwankwasiyya ba domin a tabbatar da adalci.
Mataimakin shugaban na yankin Arewa maso Yamma ya kuma zargi cewa an ware ‘yan takara da dama da ke neman tikitin Majalisar Dokoki ta Jihar, Majalisar Wakilai, Sanata da gwamna daga tsarin.
Ya ce lamarin ya haifar da rashin jin dadi a tsakanin ‘yan jam’iyyar sannan ya kai ga mika korafe-korafe a hukumance ga shugabancin jam’iyyar na kasa da Kwamitin Aiki na Kasa.
A cewarsa, kokarin shugabancin kasa na sulhunta sabanin, ciki har da taro da Kwankwaso, har yanzu bai haifar da sulhu mai dorewa ba.
Shugabannin da abin ya shafa sun dage cewa ba za a bar mutum daya ko kungiyar siyasa daya ta mamaye tsarin jam’iyyar ba, suna mai gargadin cewa hakan na iya raunana demokiradiyya ta ciki gida da hadin kan jam’iyyar.
Sai dai kungiyar Kwankwasiyya ta musanta zargin, inda ta bayyana shi a matsayin karya da rudani.
Mai magana da yawun kungiyar, Habibu Muhammed, ya ce jam’iyya ce kawai ta rika raba fom din zabe ba wata kungiyar siyasa ba.
Ya dage cewa an bude tsarin zaben fidda gwani ga dukkan ‘yan takara da suka cancanta kuma ba a hana wani dan jam’iyya samun fom din zabe ba.
Muhammed ya kara da cewa korafe-korafen sun taso ne bayan an fara zaben fidda gwani, yana mai cewa an yi adalci ga dukkan ‘yan takara.
Wani da ke kusa da Kwankwaso ya musanta zargin, yana zargin wadanda suka kai korafin da kokarin kalubalantar zabe saboda sabani na siyasa ta cikin gida.
Tushiyar ya ce an bi ka’ida wajen raba fom din zabe kuma ya bayyana zarge-zargen a matsayin na siyasa ne kawai.
Yayin da bangarorin biyu ke ci gaba da zargin juna, masu nazari kan siyasa sun yi gargadi cewa sabanin na iya kara zurfafa rarrabuwar kai a cikin NDC ta Jihar Kano sai dai idan shugabancin jam’iyyar na kasa ya shiga tsakani ya warware lamarin.












































