Dan Majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Bagwai da Shanono a Majalisar dokokin jihar Kano Ali Ibrahim Isah Shanono ya yi mi’ara koma baya wajen sake komawa jam’iyyar APC bayan ya dangwarar da shaidarsa ta NNPP.
Ta cikin wata wasika da ya aikewa da majalisar mai dauke da kwanan wata 17 ga watan Mayun da muke ciki ya bayyana komawarsa Jam’iyyar APC bayan ficewarsa kwanaki kadan.
A sanarwa da daraktan yada labara da wayar da kan jama’a na majalisar Uba Abdullahi ya fitar, ta rawaito Majalisar ta karbi wasikar tare da yi masa fatan aikhairi akan matakin.
Da yake jawabi dan majalisar ya yi alkwarin yin duk mai yiyuwa wajen samarwa da jam’iyyarsu ta APC nasara a zaben 2023 dake tafe.













































