Hukumar da ke kula da harkokin sadarwa ta Najeriya NCC, ta ce za ta hada gwiwa da babban bankin Najeriya (CBN) don dakile zamba ta yanar gizo wanda ta bayyana a matsayin babbar barazana ga ci gaban kudin zamani.
Daraktan hukumar ta NCC, Mista Efosa Idehen, shine ya bada wannan tabbacin a mahawarar da aka yi na Makarantun Sakandare na tunawa da ranar kare hakkin masu amfani da kayan masarufi ta duniya da aka yi ranar Litinin a Abuja.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa yayin da NCC ta zabi taken ta a matsayin “Ya kamata Daliban Sakandare Su Yi Amfani da Wayoyin Hannu Don Inganta Ilimi” Taken Ranar Hakkokin Masu Amfani da Kaya ta Duniya na bana shine ” Samun daidaito kan hada-hadar kudi ta zamani wato ‘Digital Finance”.
Edehen, ya ce taron zai wayar da kan jama’a da kuma ceto masu amfani da yanar gizo daga zamba ta yanar gizo da kuma wayar da kan matasa yadda ya kamata su rika amfani da tashoshi na yanar gizo wajen ayyukan kudi.
Ya ambato babban bankin na CBN yana cewa, “Zamba ta yanar gizo na janyo asarar makudan kudade a bangaren kudin Najeriya.
“Yayin da fasahar ke ci gaba da bunkasa, ana kara nuna damuwa kan yadda ake samun karuwar zamba da ake ta yaduwa a kafafen sadarwa na zamani a sassan muhimman sassan tattalin arzikin Najeriya da aka fi sani da zamba ta yanar gizo.
“Wannan barazanar da ta biyo bayan karbuwar sabbin hanyoyin yin banki ta wayar salula da sauran tsarin biyan kudi an gano ta na janyo asarar makudan kudade a kasar.
Babban bankin na CBN ya bayyana damfarar ta intanet a matsayin zamba mai hadari ga masu amfani da hanyoyin hannu wajen biyan kudi.
Daraktan ya kuma ce, a yanzu masu kutse na intanet suna kai hari ga hanyoyin sadarwa da nufin kawo cikas wajen gudanar da ayyuka da kuma kutsawa cikin bankin bayanansu.













































