Sabon Konturola na reshen jihar Kano, Sulaiman M. Inuwa, ya yi kira ga jami’an hukumar da ke kula da gidajen gyaran hali a jihar da su ba shi duk goyon bayan da ya dace da kuma hadin kan da ya dace domin cimma burin da ake bukata na hukumar.
Solacebase ta ruwaito cewa sabon Controller ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake karbar ragamar aiki daga hannun Konturola mai ritaya Suleiman T. Suleiman wanda ya shafe shekaru 35 yana aiki.
Wata sanarwa da DSC Musbahu Lawan Kofar Nassarawa jami’in hulda da jama’a reshen jihar Kano ya fitar a ranar Talata, ta ce sabon kwamandan ya yaba da goyon baya da gudumawar da dukkanin hafsoshi da jami’an rundunar suka ba shi tare da irin tarbar da suka yi masa lokacin da ya karbi mukamin Konturola.
“Ya kuma umarci mutanen jihar da su hada hannu tare da bayar da tasu gudumawa don samun nasarar aiwatar da wa’adin aikinsa.” in ji sanarwar.
‘’Ya yi kira ga jami’an hukumar da su yi aiki tare domin karfafa tsaro a jihar.












































