Kungiyar kiristoci ta Najeriya CAN ta koka kan yadda aka tsawaita rufe makarantu a jihohin Bauchi, Katsina, Kano, da Kebbi a cikin watan Ramadan, inda ta yi gargadin cewa wannan matakin ya saba wa kundin tsarin mulkin kasa, da kuma kawo cikas ga ci gaban ilimi.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar CAN Archbishop Daniel Okoh ya fitar a ranar Lahadi.
Sanarwar ta nuna matukar damuwarta kan rashin hada hannu wajen yanke shawara da kuma yadda hutun yake tasiri ga daliban da ba musulmi ba.
CAN ta jaddada cewa ilimi wani hakki ne na asali don haka ta bukaci gwamnonin jihohin da abin ya shafa da su sake duba wannan manufa domin inganta daidaito da hadin kan kasa.
Karanta: Hukumar NAHCON ta amince da yin rijistar aikin Hajji a lokacin azumin Ramadan
Kungiyar kiristoci ta bayar da hujjar cewa tsawaita hutun na kawo cikas ga jadawalin ilimi tare da kawo cikas ga kokarin samar da ingantaccen ilimi ga kowa da kowa, lura da cewa wannan rufewar na yin barazanar dagula yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a yankin, wanda matsakaicin adadin ya kai kashi 44%.
Kungiyar ta kuma bayyana rashin tuntubar masu ruwa da tsaki da suka hada da shugabannin kiristoci, iyaye, da malamai, a matsayin gazawa wajen gudanar da mulki baki daya.
Kungiyar ta CAN ta yi tsokaci kan kasashe irin su Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa, inda makarantu ke budewa a lokacin azumin Ramadan tare da daidaita jadawalin karatu, inda suke ba da shawarar a yi irin wannan tsari a jihohin arewacin Najeriya don rage matsalar ilimi.
CAN ta yi gargadin cewa za ta bi matakin shari’a idan aka kara fuskantar barazana ga ‘yancin dalibai, ciki har da kare hakkin tsarin mulki na ilimi da ‘yancin sanin ya kamata.
Kungiyar ta CAN ta kuma yi kira ga Gwamna Bala Mohammed na Bauchi da Dikko Umar Radda na Katsina da Abba Kabir Yusuf na Kano, da Nasir Idris na Kebbi da su shiga tattaunawa da kungiyoyin addini, masu makaranta, iyaye, da kuma kungiyoyin farar hula don sake duba umarnin.