Majalisar wakilai ta ƙasa ta buƙaci gwamnatin tarayya ta ɗauki matakan diflomasiyya cikin gaggawa domin tabbatar da dawowar tsohon shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan daga ƙasar Guinea-Bissau inda aka sami juyin mulki kwanan nan.
Wannan buƙata ta taso ne a zauren majalisar lokacin da mataimakin kakakin majalisa Benjamin Kalu ya jawo hankalin ’yan majalisa kan al’amari mai muhimmanci da ya shafi tsaron tsohon shugaban.
Jagoran majalisa Julius Ihonvbere ya bayyana cewa Jonathan yana Guinea-Bissau ne cikin aikin sa ido kan zaɓe na ƙasa-da-ƙasa lokacin da rikicin juyin mulki ya faru.
Ya ce Jonathan ya dade yana wakiltar ƙungiyar tattalin arzikin yammacin Afrika, ƙungiyar haɗin kan ƙasashen duniya, ƙungiyar tarayyar Afrika da Najeriya wajen sanya idanu a zaɓe a ƙasashe da dama kamar Zimbabwe, Liberia, Ghana, Mozambique, Pakistan, Tanzania da Afrika ta kudu.
Labari mai alaƙa: Tsohon shugaban ƙasa Jonathan da wasu shugabannin Afrika sun makale a Guinea-Bissau bayan juyin mulki
A yayin tattaunawa, Ihonvbere ya bayyana cewa tsohon shugaban yana cikin ƙasar a sakamakon tashin hankalin da ya barke, kuma gwamnati na sane da lamarin tare da ɗaukar matakai na musamman domin ganin ya dawo gida lafiya.
Ya jaddada cewa batun tsaron sa lamari ne da ya shafi ƙasa baki ɗaya fiye da batun juyin mulki da ya faru.
Shugaban bangaren ƙananan jam’iyyun Kingsley Chinda ya goyi bayan wannan kira tare da nuna muhimmancin rawar da Jonathan ya taka wajen gina dimokuraɗiyya da kuma kasancewarsa wakili a muhimman ayyuka na duniya.
Ya ce kulawa da tsaron duk wani ɗan Najeriya a ƙasashen waje ya zama wajibi kamar yadda ake bai wa tsohon shugaban muhimmanci.
Majalisa ta cimma matsaya ta bakin ’yan majalisa wajen buƙatar gwamnatin tarayya ta yi amfani da duk hanyoyin diflomasiyya domin tabbatar da dawowar Jonathan cikin koshin lafiya.
Wannan matsaya ta jaddada cewa tsaron ’yan ƙasa, ciki har da wadanda suka rike madafun iko a baya, na daga cikin manyan abubuwan da ya kamata Najeriya ta sanya a gaba wajen aiwatar da manufofin cikin gida da na waje.













































